Hausa

Rahama Sadau Ta Hadu Da Daliban Najeriya Dake Karatu Kasar Indiya

Shahararriyar Jarumar Fina Finan Hausa Wadda A Kwanakin Baya ta Yanke Shawarar Fara Fitowa a Fina Finan Kasar Indiya Na Bollywood Rahama Sadau Ta Gana Da Daliban Najeriya dake Karatu A Jihar Uttar Pradash Ta Kasar Indiya

Rahama Sadau Tana Tattaunawa Da Wani Ba Indiye

Rahama Sadau Ta Amsa Gayyatar Da Kungiyar Daliban Najeriya Dake Karatu A Kasar Indiya Reshen Jihar Uttar Pradash Suka Yi Mata Yayin Da ta Isa can Domin Fara Shirye Shiryen Sabon Fim Dinta

Jarumar ta Nuna Jin dadinta akan Wannan Gayyatar da Daliban suka yi Mata  Inda ta Kara da Cewa taji Dadin Wannan Gayyatar Kuma ya Nuna Alamar Cewa Daliban Suna Jin Dadin Karatu A Kasar,Shugaban Taron Malam Rakib Khan Ya Nuna Jin Dadinshi Da Amsa Kiran Da Jarumar Tayi Inda Yace Hakan na Nuna Cewa Akwai Zumunci Mai Karfi Tsakanin Hollywood Da Kannywood

Rahama Sadau Tareda Rakib Khan

Jarumar Wadda Ta Shafe Sati Biyu A Indiya Zata Fara Fitowa A Fina Finan Hollywood Nan Bada Jimawa Ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button