Hausa

A Kasuwa Nake-Jaruma Hadiza Muhammad

Shahararriyar Jarumar Fina Finan Hausa Hadiza Muhammad Ta Karyata Jita Jitar Da Ake Yadawa Cewa Ba Ta Da Niyyar Aure  A Yanzu,Inda Tace Masu Fadi. Haka Suna Fadi Ne Domin Su Kashe Mata Kasuwa

Hadiza Muhammad

Jarumar Wadda Ta Fito A Fina Finan Kannywood Fiye Da Hamsin,Tace Tayi Mamakin Jin Abinda Mutane Ke Fadi Akanta Na Cewa Bazata Yi Aure Ba A Yanzu

Nayi Mamakin Jin Haka A Matsayina Na Musulma Kuma Na Tashi  A Cikin Musulmai Nayi Aure Kuma Nasan Dadin Aure Har Kuma Na Haifi Yaya Biyu Ba Zai Yiwu Ace Bana Son Yin Aure Ba,Duk Wata Mace Ta Kirki Dama Wacce Bata Kirki Ba Tana Fatan Ace Ta Mutu A Dakin Mijinta

Banyi Tsufan Da Zaa Ce Bana Son Yin Aure Ba Saboda Haka Masu Fadin Wannan Magana Suna Son Su Kashe Min Kasuwa Ne Kuma Insha Allahu Sai Sunji Kunya Domin Ko Yanzu Na Samu Mijin Aure Zan Yi Ba Tare Da Wani Jinkiri Ba

Hadiza Muhammad

Saboda Haka Yanzu Jarumar A Kasuwa Take Kamar Yada Ta Fadi

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button