Hausa

Abdulsamad Rabiu BUA Ya Bawa Sarkin Kano Tsaleliyar Mota

Shahararren Dan Kasuwar Nan Na Jahar Kano Kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA Abdulsamad Isiyaka Rabiu Ya Gwangwaje Masarautar Kano Da Kyuatar Tsaleliyar Mota Kira Rolce Royce Ta Zamani Da Kudinta Ya Kai Naira Miliyan 200

Motar Da Aka Ba Sarkin Kano

Motar Wadda Ba Kowa Ke Hawan Ta Ba A Najeriya Ta Shiga cikin Manyan Motocin Da Sarkin Kano Mai Martaba Aminu Ado Bayero Zai dinga Hawa idan Zai Fita,Kalilan Sarakuna Ke Hawan Irin Wannan Mota A Najeriya Kuma Sarkin Kano Zai Kasance A Cikinsu

Motar Kirar Rolce Royce

Yayin Gabatar da Wannan Mota A Fadar Sarkin Kano Abdulsamad Isiyaka Rabiu Ya Ce Shi Ya Dauki Masarautar Kano A Matsayin Uwa Kuma Yana Alfahari Da Kasancewar Shi Dan Kano, Masarautar Ta Kano Ta Nuna Jin Dadinta Akan Wannan Abin Alheri Da Ya Sameta Ta Kuma Tayi Addu’ar Allah Ya Kara Ma Dukiyar Abdulsamad Albarka Ya Kuma Daga Jahar Kano Da Kuma Kasa Najeriya Baki Daya Inda Kuma Ya Kara Da Cewa Allah Ya Kawo Dauwamammen Zaman Lafiya  a Kasa Bakidaya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button