Wasanni

Abu Biyar Da Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Karawar Najeriya Da Egypt

Da Yammacin Yau Talata Tawagar Kungiyar Kwallon Kafa Ta Najeriya(Super Eagles) Zasu Hadu Da Tawagar Masar A Wasan Farko Na Gasar Cin Kofin Afirka Da Akeyi A Kamaru

Najeriya Wacce Ta Lashe Kofin Sau Hudu A Tarihi Tanada Gogaggin Yan Kwallon Da Take Alfahari Dasu Kuma Wanda Take Tunanin Zasu Kaita Gachi A Wannan Gasar,Yan Wasa Kamar Ahmed Musa,Alex Iwobi,Kelechi Iheanacho,Samuel Chukuwze Da Sauransu Sune Ake Tunanin Zasu Iya Taka Rawar Gani A Wasan Da Za’a Buga A Garoua

Su Kuma Egypt Suna Da Nasu Yan Wasan Kamar Muhammad Salah Na Liverpool Da Kuma Muhammad Elneny Dake Buga Wasa A Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Dake Ingila

Abu Biyar Da Ya Kamata KusaniĀ 

Najeriya Ta Lashe Kofi Hudu A Tarihi Gasar

Kasar Masar Tafi Kowace Kasa Lashe Gasar A Tarihi(7)

Wannan Itace Gasar Kwallon Afirka Ta Karshe Da Kyaftin Din Najeriya Ahmed Musa Zai Buga

Wannan Ne Karo Na Farko Da Sabon Kocin Najeriya Zai Jagoranci Tawagar

Najeriya Ta Samu Tagulla A Shekarar 2019 Bayan Ta Doke Kasar Tunisiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button