"
Hausa

Allah Ya Yiwa Sarkin Gaya Alh Ibrahim Abdulkadir Gaya Rasuwa

Allah Ya Yiwa Mai Martaba Sarkin Gaya Alh Ibrahim Abdulkadir Gaya Rasuwa Ayau Laraba 22 Ga Watan Satumba Bayan Fama da Gajeruwar Jinya Sakamakon Rashin Lafiya da Yayi Fama da ita

Kafin Rasuwarshi Ya Kasance Sarkin Gaya Na Tsawon Shekaru Fiye Da Ashirin Inda Ya Gaji Mahaifinsa Sarkin Gaya Na Lokacin Alh Abdulkadir Gaya,Ya Rasu Ya Bar Mata Uku Da Yaya Da Jikoki

Marigayi Abdulkadir Ibrahim Gaya Sarki Ne Mai Daraja Ta Daya A Cikin Sarakunan Kano Kuma Mai Fada Aji a cikin Masarautar Kano,Mutuwar tashi tazo Sati Uku Bayan Mutuwar Mai Martaba Sarkin Sudan Na Kwantagora Alh Saidu Namaska Wanda Shima Babban Sarki Ne A Arewacin Najeriya

Sarkin Gaya Alh Ibrahim Abdulkadir Gaya

Muna Addu’ar Allah Ya yi Mishi Rahama Ya Kuma Sawa Abin Da Ya Bari Albarka,Allah Kuma Ya Bawa Iyalinsa Hakurin Wannan Babban Rashi Da Sukayi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button