"
Hausa

Arsenal Ta Fara Premier League Na Bana Da Kafar Hagu

Kungiyar Kwallon Kafa Dake Buga Kofin Kalubale Na Premier League Arsenal Ta Fara Wannan Kakar Wasannin Ta Bana Da Kafar Hagu Bayan Tasha Kashi A Hannun Abokiyar Karawar ta Brentford Ranar Jumaa

Arsenal Wacce Ta Kare A Mataki Na Takwas Bara Ta Ziyarci Brentford Domin Bude Wasannin Kakar Kwallo Ta 2021/2022 Amma Bata Sha da dadi ba yayin da masu masaukin  Baki suka Yi Nasara Da Ci 2:0

Dan Wasan Brentford Canos Ne ya Fara Cin Kwallo a minti na 22 da Fara Wasa kafin Noergaard ya kara ta biyu Bayan an dawo daga hutun Rabin lokaci

Kocin Arsenal Ya Ajiye Wasu Daga Cikin Yan Wasansa Ciki Harda Kyaftin din Kungiyar Dan kasar Gabon Piere Emeric Aubameyang Da Kuma Andre Lacazette Domin tunkarar Kungiyar kwallon Kafa ta Chelsea a Wasan mako na biyu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button