Jarumar Fina Finan Kannywood Fati Washa Ta Magantu Akan CeCe Kucen Da Akeyi Dangane Da Ficewar Nafisa Abdullahi Daga Shirin Labarina Na Malam Aminu Saira
Jarumar Yayin Zantawa Da Yan Jarida Ta Fadi Cewa Zuwa Yanzu Babu Wani Wanda Ya Tuntubeta Akan Ko zata Amince Ta Fito A Matsayin Jaruma Nafisa Abdullahi Wacce Ta Fita Ana Tsaka Da Yin Shirin

A Kwanakin Baya Dai Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Sanar Da Ficewarta Daga Shirin Labarina Saboda Dalili Na Kashin Kai Lamar Yada Ta Fadi A Cikin Wata Takardar Data Rubutawa Darakta Malam Aminu Saira
Tun Lokacin Ake Neman Wace Zata Maye Gurbinta,Hakan Yasa Mutane Ke Ganin Babu Wata Wacce Ta Cancanci Maye Gurbin Nafisa Abdullahi A Cikin Shirin Labarina Kamar Fatima Abdullahi (Fati Washa)