"
Hausa

Bani Kadai Bane Akwai Sauran Mutum Shida-Dan Fashi

Wani Mutum Da Aka Kama A Jihar Nasarawa Yana Kokarin Tsallaka Iyaka Zuwa Jihar Filato Da Makamai Ya Bayyana Cewa Ba Shi Kadai Bane Akwai Mutum Shida Suna Kan Hanya

Likita

Wani Mutum Dan Kimanin Shekaru 35  Ya Shiga Komar Rundunar Yan Sandan Jihar Nasarawa Bayan Sun Yi Nasarar Cafke Shi Yana Yunkurin Tsallakawa Makwabciyar Jihar Filato Da Miyagun Makamai Da Suka Hada Da Bindiga Kirar Ak 47 Kimanin 40 Da Kuma Alburushi Fiye Da Dubu Biyu Sai Kuma Magazines Kwara 54

Magazine Din Da Aka Sameshi Dasu

Likita Kamar Yada Yace Ana Kiransa Ya Fada Wa Jamian Tsaro Cewa Ba Shi Kadai Bane Ke Da Niyyar Shiga Filato Da Makamai Ba Akwai Wasu Mutum Shida Suma Suna Kan hanyar su ta Shiga Da Miyagun Makamai Jihar Ta Filato

Jihar Filato na fama da Rikece Rikecen Addini Inda A Kwanan Nan Wasu Wayanda Ake Zaton Mabiya Addinin Kirista Ne Suka Kashe Musulmai Fiye Da 20 A Yankin Kudancin Jihar

Wanda Hakan Yasa Sufeto Janar Na Yan Sandan Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro A Yankin Domin Gujewa Matsalar Da Ka iya Biyo baya

Yanzu Haka Rundunar Yan Sandan Jihar Nasarawa ta garkame Mutumin Har Sai Bayan Ta Kammala Bincike Kafin A Tasa Keyashi Zuwa Kotu Domin Yanke Mishi Hukuncin Da Ya Dace Dashi

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button