Hausa
Bazan Saka Yata A Harkar Fim Ba- Sani Danja

Shahararren Jarumin Fina Finan Kannywood Sani Musa Wanda Akafi Sani da Danja Ya Bayyanawa Duniya Cewa Bazai Amince Yarsa Ta Fara Fitowa a Fina Finan Kannywood Ba Kamar Yada Sauran Yan Fim Kanyi Na Su Saka Yayansu A Harkar
Danja Yayi Wannan Bayani Ne Yayin Ganawa Da Manema Labarai Inda Yace Yarsa Iman Ba Yar Fim Bace Kawai Zatayi Karatu Kafin Lokacin Auren Ta Yayi Ya Aurar Da Ita
Danja Wanda Ya Shafe Shekaru Goma Sha Biyar A Harkar Fim Ya Kuma Auri Jaruma Mansura Isah Kuma Allah Ya Azurta Su Da Haihuwar Kyakkyawar Yarsu Iman
Harkar Fim Wata Hanya Ce Da Mutane Kanbi Wajen Fadakarwa,Ilmantarwa,Nishadantarwa Da Kuma Yada Manufofi Ta Hanyar Shirya Fim