Hausa

Bet9ja:Tasirin Cacar Kwallon Kafa A Arewacin Najeriya

Caca haramun ce a Musulunci Wanda Hakan Yasa ba’a Tunanin samun Wani musulmi da yin Caca Amma Kash an Samu Wasu Daga cikin Musulmai sun Bari Shedan ya ribace su har Yasa sun Fada Cikin Wannan mummunar dabia ta caca

Bayan karta da muka Sani a matsayin Babbar caca yanzu an Samu Wata kalar Cacar wato Bet9ja Wanda Wani Kamfanin Najeriya ke Shiryawa a Duk lokacin da za’a yi Wasan Kwallon Kafa anan gida Najeriya Dama kasashen ketare

Yada ake yin Cacar Bet9ja shine Mutum zai yi hasashen yada Zata Kaya a Tsakanin Kungiyoyi biyu da Zasu fafata a Wasa wato zaka Fadi yada za’a tashi Wasan Bayan minti 90 na kowace Kwallo Bayan an tashi Kwallo Sai su Duba hasashen ka idan kayi daidai shine za ka Karbi Makudan Kudade Daga garesu idan Kuma baka yi daidai ba shikenan ka fadi

Ba kyauta ake buga cacar Bet9ja ba zaka saka kudi adadin karfinka Daga Naira 100 Zuwa 1,000,000 Wanda Inka yi hasashen daidai zasu ninka maka Abin da kasaka

Tambarin Bet9ja

Nayi wannan Rubutun ne Domin Ganin yadda Wannan dabia ta Fara yin kamari a Tsakanin Matasan mu Na Arewa,So da dama Saboda Neman ayi Kudi a dare Daya Kan sa Wasu yin Wannan caca ganin Ana samun Kudi sosai idan Akayi Sa’a,Wasu Kuma Suna ganin Cewa Wannan Wata hanya ce da Mutum zai Dinga ninka samunsa Duk Karshen mako

Na Sha Ganin Matasa a Gidan Kallon Kwallo Suna Kuka idan Wata Kungiyar Tayi nasara akan Abokiyar karawarta Sai Nake Tunanin ko Dama Wannan Mai kukan Yana Goyon Bayan Kungiyar da tasha kashine,Daga Baya Sai Nagane Ashe ba Haka Abin yake ba Dalilin kukan shine don hasashen da Yayi a katin Cacar sa Bai Zo daidai ba

Ina Ganin ba Wannan ne hanya mafi sauki da Matasan mu zasu Samu kudaden Shiga ba Akwai ayyuka da Dama Wanda zasuyi su Samu kudinsu ba tare da Wata tsangwama ko fargaba ba,Saboda kamar yada Wani mawaki ke Fadi a cikin wakarsa Cewa Dan Caca Barawo Ne Ko Bai Taba Sata Ba,Kenan akoda yaushe idan ka rasa kudin bugawa zaka iya zuwa ka yi Sata

Ita Wannan caca ta Bet9ja Tana da Wani Abu Wanda kusan Duk Mai yinta ya San da Wannan Abu ba komai bane illa Faduwa Bayan Nasara Wato Bayan ka buga katinka Sai kaje ka rike Shi Kuma ka Dinga dubawa akai akai don Ganin halin da ake Ciki,So da Dama Sai kaga Wasan farko ya Shiga Kuma kana sa ranka da cewa Sauran wasannin ma zasu Shiga Amma Sai daga Baya Sauran su Kasance ba yada aka yi Tsammani ba wanda Hakan na Kawo damuwa sosai Wanda Kuma damuwa matsala ce ga lafiyar Dan Adam

Ina sa ran Iyaye zasu lura da Yayansu dake Kallon Kwallo don kada ya Kasance kana Tunanin Kallon Kwallo kawai danka Yake Amma Kuma a Bayan fage Yana buga Cacar Bet9ja

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button