Hausa

Cikakken Tarihin Bobrisky Namijin Da Ya Mayar Da Kanshi Mace

Ba Kasafai ake samun Wani mutum yaji Baya son halittar da ya wayi gari ya ganshi da ita  ba Amma a Wasu lokutan Ana samun namiji yaji Cewa Ina ma an halicce a Matsayin Mace ko Kuma Mace taji Cewa Ina ma Ace Tazo Duniya a Matsayin Namiji,Ana samun irin haka idan Mutum yaga Cewa Akwai Wani Abu,da Wanda ba jinsin su daya ba yake yi Wanda Shi Baya iya yin Irin wannan Abu

Misali Idan Namiji yaga Cewa Mace zata iya yin laifi a sassauta Mata Wurin yi Mata hukunci,Inda a Kasar jamus Ana Yanke Ma Mace Rabin Hukuncin da aka Yanke ma Namiji Koda Kuwa laifin su daya,To a Irin Wannan yanayi idan Namiji Ya tsinci Kanshi ya aikata wani laifi Sai Yaji Cewa ina ma Ace Shi Macece Domin a rage masa Hukunci Akan  abin da ya aikata

Ita Kuma Mace a Wasu lokutan zataga Cewa Namiji Yana da ikon da Zai fita Yayi rayuwar Shi a cikin Mutane sabanin Mace da A Kowane Lokaci anfi  son ta Kasance a Gida batare da ta fita Wajeba

Wannan da Kuma Wasu dalilai na Daga cikin abin da Ke sa Wasu tunanin canza halitta Daga jinsin da Suke,Zuwa wani jinsi daban Duk da hatsarin Dake tattare da Hakan

A Yau Mun Zo maku da Tarihin Wani Olanrawaju Okuneye Idris Wanda Aka Fi Sani Da Bobrisky Mutumin Da ya maida Kanshi Mace ta hanyar Canja Kwayoyin Halitta

Bobrisky

Kamar Yada Kuka Gani A Sama Sunanshi Olanrawaju Okuneye Idris Wanda Aka Haifa a Yankin Metta Dake Jihar Legas,An Haifi Shi Ranar 31ga watan Agusta Shekara ta 1991 Yayi Karatun Boko A Shahararriyar Makarantar Nan Dake Lagos Kings College Kafin Ya Wuce University Of Lagos Domin Cigaba Da Karatu

Bobrisky

Bayan Kammala Karatu Bobrisky Ya Fara Tunanin canza Halitta Zuwa Mace Inda Ya Tafi Kasar Turai Domin Cika Wannan Buri Nasa

A Shekarar 2019 Ya Fada Ma Duniya Cewa Daga Yanzu A Dinga Kiranshi Da Inkiyar Ita A Madadin Shi Da Aka Saba Kiransa

Ya Janyo Cece Kuce  A Kafafen Sada Zumunta Tun Bayan Ayyana Kansa A Matsayin Mace Inda Wasu Ke Ganin Abin Da Yayi Bai Dace Ba Wasu Kuma Ke Ganin Wannan abun Ba Komai Bane A Kasar Da Babu Doka A Kan Hakan

Shugaban Sashen Kula Da Al’adu A Ma’aikatar Matasa Da Al’adu Otunba Olusegun Ya Kira Bobrisky A Matsayin Abin Kunya Ga Kasa Inda Yaja Hankalin Matasa Akan Su Gujewa Aikata Kwatankwacin Abin Da Ya Aikata

Tun Bayan Zaman Bobrisky Mace Hakan Ya Janyo Mashi Suna Inda Kamfanoni A Ciki Da Wajen Najeriya Ke Tallata Hajar su Da Suna Ko Hoton Bobrisky Inda Suke Bashi Makudan Kudi Domin Yi Musu Tallace Tallace

Bobrisky 

Hakan Yasa Bobrisky Samun Makudan Kudade Da Yasa Darajar Kudinsa Ya Kai Miliyan  3.125 Na Dalar Amurka Kwatankwacin Naira Biliyan Daya Da Doriya

Alh Musibau Okuneye Shine Mahaifin Bobrisky,Dan Asalin Jahar Ogun

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button