Hausa

Cikakken Tarihin Mawaki Hamisu Breaker

Hamisu Saidu Yusuf Wanda Akafi Sani Da Hamisu Breaker ba boyayyen Mutum bane a Masana’antar Kannywood Dama Duniya Baki Daya,Ya Shahara a Fannin Waka Inda Ya Zamo Mawakin da yafi Shahara A Dan Kankanin Lokaci A Tarihin Masana’antar Kannywood

Hamisu Breaker

Breaker Haifaffen Garin Kano Ne,An Haife Shi a Unguwar Dorayi Dake Cikin Kwaryar Birnin Kano,A Shekarar 1992 Yayi Makarantar Firamare Da Sakandire duk a Kano Kafin Ya Fara Harkar Waka

Hamisu Saidu Yusuf (Breaker) Yayi Karatun Boko Dana Muhammadiyya Tun Yana Yaro Kafin Ya Shiga Harkar Waka

Ya Zama Shahararre A Fannin Waka tun lokacin da ya saki wakar Shi ta Farko a Shekarar 2019,Hamisu Yayi Waka Fiye da 100  a Shekaru uku da Yayi a Kannywood

Kadan Daga Cikin Wakokin da yayi akwai Ashe Da Rai,Masoyan Juna,Kar Ki Barni Da Sauransu,Wakar Shi Ta Baya Bayan Nan Ashe Da Rai Ta Kasance Wakar Hausa Da Akafi Saurare A YouTube A Tarihin Kannywood

Hamisu Saidu Yusuf

Zuwa Yanzu Dai Hamisu Breaker Baida Aure Amma Yana Da  Niyyar Yi Idan Allah Ya Kawo Lokaci,Kafin Ya Fara Harkar Waka Hamisu Ya Kasance Yana Dinki A Wani Shago Dake Nan Unguwarsu Ta Dorayi A Kano

Da Aka Tambayeshi Kan Abin Da Ya Jawo Hankalin Shi Har Ya Fara Yin Waka Hamisu Yace Sha’awa ce Tasa Ya Fara Waka

Tun Ina Yaro Na Fara Yin Waka A Makarantar Mu Inda Yara Yan Uwana Su Kanyi Kida Ni Kuma Inyi Waka Amma Ban Taba Tunanin Zan Zamo Mawaki Ba Ko Kuma In Dauki Waka A Matsayin Sana’a Ba Sai Yanzu Dana Girma Nagane Cewa Allah Ya Bani Basirar Yin Waka,Sai Nayi Amfani Da Ita Wurin Fadakar Da Mutane Da Kuma Ilmantarwa

– Hamisu Breaker

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button