Daga Karshe Ummi Rahab Ta Maka Adam Zango Kotu

Tun Bayan Korar da Furodusan Fim din Farin Wata Adam Zango Ya yiwa Matashiyar Yar Fim Ummi Rahab daga cikin Fim din nashi, rigima ta barke a Tsakanin su Inda kowa Ke Ganin Akwai lauje cikin Nadi Ganin Cewa sun Dade Suna tare da Adam Zango
Adam Zango Yakasance Maigidan Ummi Rahab a Harkar Fim Shekaru da dama Inda Ya Fara sakata a Fim Din Ummi tun Tana Yar Shekara Goma a Duniya

Adam Zango ya Fadi dalilin da Yasa ya cire ta Daga Fim din Farin Wata Inda Yake Cewa a Matsayinshi Na Maigidanta A Harkar Fim Yana Son ya Bata Tarbiyya Amma Tana Bijirewa

Da Take Mayar Da martani dangane da Abin da Zango Ya Fadi Ummi Tace Idan Ya Cigaba Da Yunkurin Bata Mata Suna Zata Tona Asirinshi
Hakan Yasa Mutane Sukayi ta tofa Albarkacin bakinsu a Shafukan Sada Zumunta Inda Wasu Ke Ganin Wannan Rikicin Da Ya Barke A Tsakanin Jaruman Nada Alaka da Maganar Da Ita Ummi Tayi Nacewa A Wannan Fin Din Na Farin Wata Da Tafito Naira 15,000 Adam Zango Yabata A matsayin Sallama
Yanzu Dai Ummi Da Yan Uwanta Sun Shigar Da Kara A Wata Kotun Majistire Dake Jahar Kano Inda Suke Zargin Adam Zango Da Yunkirin Bata Wa Matashiyar Jarumar Suna