Hausa

Dan Najeriya Ya Zama Mataimakin Shugaban Hukumar Yan Sanda Ta Duniya

Mataimakin Sufeto Janar Na Yan Sandan Najeriya AIG Garba Baba Umar Psc.Ya Samu Nasarar Zama Mataimakin Shugaban Hukumar Yan Sanda Ta Duniya INTERPOL Reshen Afirka

Ya Samu Wannan Nasara Mai Dunbin Tarihi Bayan Ya Lashe Zaben Da Aka Gudanar A Kasar Turkiyya Da Tazarar Kuri’u Masu Yawa,Taron Wanda Shine Taro Na 89 Da Babbar Kungiyar Ta Yan Sanda Ta Gudanar,Ya Samu Halartar Ministan Harkokin Yan Sanda Na Najeriya Muhammad MaigariĀ  Dingyadi,Shugaban Hukumar Yan Sandan Najeriya Baba Usman Alkali Psc + Da Kuma Babban Hafsan Sojojin Ruwa Na Najeriya Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo Da Kuma Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa Da Yiwa Tattalin Arziki Zagin Kasa (EFCC) Malam Abdulrashid Bawa

Wannan Zabe Da Aka Gudanar Ya Zama Babbar Nasarar Ga Najeriya Inda Zata Kara Samin Dama Wajen Kawo Karshen Yan Bindiga Masu Tada Kayar Baya Da Sache Sachen Bayin Allah

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button