Hausa

Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Rabawa Sojoji Motoci Masu Sulke Don Yakar Yan Bindiga A Fadin Jihar

Gwamnatin Jihar Kebbi Karkashin Jagorancin Gwamna Sanata Atiku Abubakar Bagudo Ta Kaddamar Da Motocin Yaki Masu Sulke Guda Goma Inda Ta Rabawa JamianĀ  Sojojin Dake Jihar A Yunkurin Da Ta Ke Na Ganin Karshen Yan Bindiga A Fadin Jihar

Mataimakin Gwamnan Kanal Yombe Dabai Ne Ya Wakilci Gwamnan A Wurin Raba Motocin A Fadar Gwamnatin Jihar Dake Birnin Kebbi

Daya ke bayani a Wurin taron kanal Yombe Yace Wannan Matakin Da Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Dauka Wani Shiri Na Ganin Bayan Yan Tada Kayar Baya Dake Damuwar Wasu Yankun Jihar Musamman Yankin Karamar Hukumar Zuru

Motocin Da Gwamnati Ta Raba

Yace Zaman Lafiya Shine Ginshikin Ci Gaban Kowane Yanki Saboda Haka Gwamnatin Ta Dauki Wannan Matakin Domin Karfafa Wa Jamian Tsaro Gwiwa Wajen Yaki Da Taadanci A Fadin Jihar

Motoci Masu Sulke

Jihar Kebbi Dake Yankin Arewacin Najeriya Na Fama Da Hare Haren Yan Bindiga A Yan Kwanakin Nan Abin Da Baa Saba Gani Ba A Baya

Masu Hasashe Na Ganin Makwabtakar Jihar Da Jihar Zamfara Inda Abin Yafi Kamari na Daga Cikin Dalilan Daya Sa yan Bindiga Ke Cigaba da Kai Hare Hare A Wasu Yankunan Jihar

Abaya Dai Gwamnatin Jihar Ta Dauki Matakin Sasantawa Da Yan Bindiga Amma Hakan Yaci Tura,Hakan Yasa Gwamna Atiku Abubakar Bagudo Ya Dauki Wannan Matakin Domin Magance Matsalar Tsaro A Fadin Jihar

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button