Hausa
Hotunan Shagalin Kamun Yar Sarkin Bichi Zahra Nasiru Ado Bayero

Yau Alhamis Akayi Bikin Aladar Kamu A Shirye Shiryen Bikin Zahra Nasiru Ado Bayero Da Yusuf Muhammadu Buhari Wanda Zaayi Ranar Juma’a 20 Ga Watan Agusta
Aladar Kamu Na Daya Daga Cikin Shagulgulan Aure Da Akeyi A Kasar Hausa Inda Amarya Zata Ci Ado Ta Tafi Wurin Yan Uwa Da Abokan Arziki Domin Yin Bankwana Da Kuma Neman Shawarwari A Wurin Manya

Akanyi Wannan Biki A Jajibiren Daurin Aure,Zahra Nasiru Ado Bayero Ya Ce Ga Mai Martaba Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero Kuma Jika Ga Tsohon Sarkin Kano Ado Bayero

Za’a Daura Auren Masoyan A Fadar Sarkin Bichi Ranar Juma’a 20 Ga Watan Agusta

Auren Zai Samu Halartar Manyan Mutane Daga Ciki Da Wajen Najeriya