"
Hausa

Inason In Taka Matsayin Da Mahaifina Ya Taka-Hanafi Ibro

Da Ga Shahararren Dan Wasan Barkwanci Rabilu Musa Ibro Hanafi Into Ya Bayyana Cewa Yana Son Ya Taka Matsayin Da Mahaifina Marigayi Rabilu Musa Ibro Ya Taka

Matashin Dan Wasan Kwaikwayo Hanafi Ibro Ya Fito Ya Fada Wa Duniya Cewa Yana Fatan Nan Gaba Duniya Zata Sanshi Kamar Yada Tasan Marigayin Mahaifinsa A Harkar Barkwanci

Hanafi Rabilu Musa Ibro

Hanafi Mai Shekaru 28 A Wata Hira Da Yayi Da Kafar Watsa Labarai Ta BBC Hausa Ya Bada Kadan Daga Cikin Tarihinsa Inda Yace Yayi Makarantar Firamare Da Sakandare Kafin Ya Fara Harkar Fim,Inda Kuma Ya Cigaba Da Cewa Ya Shiga Harkar Fim Bayan Mahaifinsa Rabilu Musa Ibro Ya Rasu

Zuwa Yanzu Dai Hanafi Ya Fara Fitowa A Fina Finan Kannywood Musamman Na Barkwanci Domin Cike Gurbin Da Mahaifinsa Rabilu Musa Ibro Ya Bari A Masana’antar  Ta Kannywood

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button