Hausa

Janyo Malamai A Harkar Siyasa-Daidai Ko Rashin Daidai

Kwanan Nan Mai Girma Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Ya Nada Shahararren Malamin Addinin Musulinci Malam Ahmed Suleman Kano A Matsayin Karamin Kwamishinan Ilmi Na Jihar Kano,Inda Kuma Nan Take Ya Shiga Ofis Ya Fara Yiwa Alummar Jihar Kano Aiki

Sanya Malamai A Harkar Siyasa Ba Sabon Abu Bane A Najeriya Tun Lokacin Da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Nada Dr Sheikh Ali Isah Pantami A Matsayin Ministan Sadarwa Na Najeriya,Abunda Ya Ja Hankalin Mutane Suka Tofa  Albarkacin Bakinsu Akan Matakin Da Shugaban Ya Dauka Na Mallakawa Malamin Addinin Ma’aikata Sukutum

Wasu Na Ganin Yin Hakan Zai Hanawa Malamin Cigaba Da Fadakarwa Saboda Aiki zai  Mishi Yawa Yayinda Wasu Kuma Ke Ganin Anyi Hakanne Domin Hana Malamai Sukar Lamirin Gwamnati Idan Tayi Wani Abin Da Bai Kamata Ba

Yanzu Kuma Da Gwamnatin Jihar Kano Karkashin Jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje Ya Nada Ahmed Suleman Kwamishinan Ilmi Ana Hasashen Hakan Zai Kara Bude Wata Dama Da Malamai Zasu Shiga Harkar Siyasa Tsundum Ba Tare Da Wata Tangarda Ba,Wanda Kuma Hakan Ka Iya Jawo Su Malaman Su Daina Fadawa Shugabanni Gaskiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button