Hausa

Jaruman Kannywood Da Sukafi Kudi A Shekarar 2021

Masana’antar Kannywood Wurine da Mutane kan Tafi domin Nuna basirar da Allah Ya Basu ta hanyar Nishadantarwa,Ilmantarwa da Kuma Wa’azantarwa,Bayan haka Wurine da zaka Samu Makudan Kudade Ta hanyar fitowa a Fina Finai da Kuma Tallace Tallace

Wani Lokaci Mutane Kan yi gardama akan Wanda Yafi samun Kudi a Tsakanin Mawaki Da Kuma Jarumin Kannywood,A Yau Zamu Kawo maku Jerin Jaruman da suka fi Kudi A Masana’antar Ta Kannywood Sai Kuyi Alkalanci Da Kanku

4 Sani Musa Danja

Sani Musa Danja

Shahararren Jarumin Wasan Hausa Sani Musa Danja Shine Mutum Na Hudu A Jerin Mu Na Wannan Shekara,Jarumin Yayi Suna A Shekarun Baya A Harkar Fim,Duk Da Ya Daina Fitowa A Fina Finai Inda Ya Koma Tallace Tallace,Siyasa Da Kuma Jakadanci

Sani Musa Danja Shine Mijin Tsohuwar Jarumar Kannywood Mansura Isah,Sani Ya Bude Kamfanin Shirya Fina Finan Kannywood 2 Effect Empire Tare Da Abokinsa Yakubu Muhammad A Shekarar 2007,Inda Kamfanin Yayi Zarra A Shirya Manya Manyan Fina Finai Irinsu,Zo Kiji, Dan Zaki,Gidan Danja,Fanan Da Sauransu

Bayan Harkar Fim Sani Yana Tallata Hajar Kamfanin Sadarwa Na Glo Da Kuma Kamfanoni Irinsu Maggi Da Sauransu

Darajar Dukiya: #250,000,000

3 Yakubu Muhammad

Yakubu Muhammad

Jarumi Yakubu Muhammad Ya Fara Waka Kafin Ya Koma Harkar Fim Inda Ya Rera Waka Fiye Da 100

Tareda Abokinsa Sani Danja Suna Da Kamfanin Shirya Fina Finai,Kuma Ya Fito A Fina Finai Da Dama Wanda Suka Hada Da Gidan Danja,The North,Sons Of The Caliphate da Sauransu Yakubu Na Daga Cikin Yan Wasan Kannywood Kalilan Dake Fitowa A Fina Finan Nollywood,Kamar Sauran Yan Fim Yakubu Jakada Ne Ga Kamfanin Sadarwa Na Glo

Darajar Dukiya: #280,000,000

2 Adam A Zango

Adam A Zango 

Wani Shahararren Jarumin Kannywood Da Muke Dashi A Jerin Masu Kudi Shine Adam A Zango,Haifaffen Zangon Kataf A Kaduna Adam Yana Daga Cikin Jaruman Kannywood Da Sukafi Yawan Masoya A Fadin Duniya

Dukiyar Zango Ya Same Tane A Harkar Fim Wanda ya Shefe shekaru Yana Yi, Dukiyar Zango Ta Kara Fitowa Ne Bayan Da Ya Dauki Nauyin Karatun Wasu Dalibai A Kaduna Inda ya Bada Zunzurutun Kudi Har 47,000,000 A Shekarar 2018

Darajar Dukiya: #300,000,000

1 Ali Nuhu

Ali Nuhu

Mutum Na Farko A Wannan Jadawali Na Masu Kudi A Kannywood Shine Ali Nuhu

Sarki Ali Kamar Yanda Ake Kiransa Yayi Shekaru Fiye Da Ashirin Yana Sana’ar Wasan Kwaikwayo Ya Shahara A Wannan Fannin Inda Ake Ganin Yafi kowa samun Nasarori A Tarihin Kannywood

Shine Mutum Na Farko Da Ya Fito A Fina Finan Kannywood Da Nollywood,Kuma ya Samu digirin girmamawa Daga Wata Jamia A Kasar Benin

Ali Nuhu Ya Fito A Fina Finai Fiye Da 500 Kuma Yanada Nasa Kamfanin Shirya Fina Finai Mai Suna FKD Production

Bayan Harkar Fim Ali Nuhu Jakada Ne Na Kamfanoni Daban Dabam Da Suka Hada Da Glo, Samsung,Coca Cola Da Sauransu,Kuma Ya Kasance Ambasada A Jamiar Greenfield University

Darajar Dukiya: #450,000,000

Sanarwa!!!

Wannan Jadawali Mun Tattaro Shine Daga Kididdiga Da Kuma Hasashe Bai Zama Lallai Ne Abin Da Muka Rubuta Shine Dukiyar Su Ba

Mungode

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button