"
Hausa

Jaruman Kannywood Da Sukafi Yawan Mabiya A Shafinsu Na Instagram

Masana’antar Kannywood Tayi Fice A Afirika Wajen Nishadantar Da Alumma Da Shirye Shiryensu Wanda Hakan Yasa Jaruman Kannywood Sukayi Suna Anan Gida Najeriya Dama Sauran Kasashe

A Yau Zamu Duba Manyan Jaruman Da Sukafi Yawan Mabiya A Shafin Sada Zumunta Na Instagram

Shafin Instagram Wurine Da Aka Tanada Domin Yada Hotuna Da Tallace Tallace Wanda Hakan Yasa Jaruman Suka Mayar Da Shafin Wani Dandali Na Yada Hotunansu

Ali Nuhu

Jarumi Na Farko A Yawan Mabiya Shine Ali Nuhu Wanda Akafi Sani Da Sarki Ali,Yanada Yawan Mabiya 2.3m Jarumin Wanda Akeyiwa Kallon Bahaushe dayafi shahara a duniyar Fina finai shine Mai kamfanin shirya Fina finai na FKD Production

Hadiza Gabon

Jaruma Hadiza Gabon Tazo Ta Biyu a jerin masu Mabiya inda take Da Mabiya 2.2m jarumar Yar asalin kasar Gabon Tayi Suna Ne a shekarar 2017

Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi itace ta uku yayinda take Da Mabiya 1.9m Nafisa Itace Jarumar data fito a matsayin Sumayya A fim din mako mako na Labarina Tayi Fice a harkar fin a shekarar 2015 a fim din Sai Wata Rana

Maryam Booth (Dijangala)

Maryam Dijangala Tana daga cikin matan da tauraruwar suke Ke haskawa a Kannywood tun fim dinta na Farko Dijangala ta cigaba da fitowa a Fina finai da dama dakuma Tallace Tallace Wanda yanzu haka Itace Jakadiyar Magi Ajino Moto A Najeriya Tana da mabiya 1.8m

Maryam Yahaya

Jaruma Maryam Yahaya Ba Bakuwa bace a harkar fin tun bayan fitowar ta a fim din Rariya Tana da mabiya 1.6m a shafinta

Naziru M Ahmad

Naziru Sarkin Waka Kamar Yada Aka fi saninshi mawaki ne da Yayi Suna a wakar aure Wanda Shima yaje da mabiya 1.4m a nashi Shafin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button