Hausa

Jarumar Kannywood Ta Fara Fitowa A Fina Finan Indiya

Shahararriyar Jarumar Fina Finan Hausa Kuma Furodusa Jaruma Rahama Sadau za ta Fara Fitowa a Fina Finan Bollywood Dake Indiya Inda ta Fara Daukar wani fim da Zai fito Nan Bada dadewa ba

Jaruma Rahama Sadau Tare Da Abokiyar Aikinta

Rahama Sadau ta Dade Tana Fitowa a fina finan da ba Kannywood ba,Zuwa yanzu Rahama Sadau ta fito a fina finan Nollywood na Kudancin Najeriya fiye da biyar,Daga cikinsu Akwai Up North da Kuma Sons of the Caliphate

Yanzu Haka Dai Ana Shirye Shiryen fitowar Fim din da ita Jarumar Zata fito a Matsayinta na Mai Taimaka Wa Babbar Jaruma,Rahama ta Kasance Daya daga cikin Jaruman Kannywood da suka iya yare Dabam Dabam Ciki har da indiyanci

Rahama Sadau

Ta Rubuta a Shafin ta na Facebook Cewa Tana Farin cikin haduwa da Jarumar Indiya Wadda za su fito a Fim din tare

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button