Hausa
Kar Ka Kara Saka Wannan Tufafin-Umarnin Joji Ga Nmadi Kanu

A Yau Talata18 Ga Watan Janairu Ne Aka Cigaba Da Shari’ar Dan Gwagwarmayar Kafa Kasar Biyafara Mazi Nmadi Kanu Wanda Ya Shafe Watanni A Tsare A Wurin Jami’an DSS
Karar Wacce Aka Dade Anayinta Ana Zargin Nmadi Kanu Da Laifin Cin Amanar Kasa Tareda Neman Tada Zaune Tsaye A Lokuta Da Dama,Lauyan Wanda Ake Kara Mike Ozekhome Ya Zargi Jamian DSS Da Takurawa Wanda Yake Karewa Da Kuma Hanashi Abinci da Damar Yin Ibada Cikin Kwanciyar Hankali
Mai Shari’a Binta Nyako Ta Umarci Jami’an DSS Da Su Dinga Barinshi Yana Ibada Da Wanka Saboda Bata Bukatar Ta Kara Ganinshi A Cikin Kayansa Na FENDI Wanda Ya Dade Dasu Ajikinsa Tun Lokacin Da Ya Dawo Najeriya Daga Kasar Waje

Ana Fatan Yau Za’a Yanke Masa Hukunci Bayan Doguwar Shari’ar Da Aka Dade Anayi