Hausa

Mabiya Sun Lakadawa Fasto Duka Akan Biyan Kudi

Wasu Mabiyan Addinin Kirista Sun Fusata Da Maganar Fastonsu Har Ta Kai Ga Sun Lakada Masa Dan Banzar Duka A Wani Gari Da Ake Kira Empu A Kasar Kenya

Fasto James Mugo Wanda Shine Babban Limamin Cocin Wings Of Blessings Ya Hadu Da Fushin Mabiyansa Bayan Ya Nemi Su Biya Zunzurutun Kudi Har Ksh 4200 Kwatankwacin Naira 16000 Idan Suna Son Su Samu Albarkar Sabuwar Shekara

Fasto James Mogu A Gadon Asibiti

Amma Sunyi Kunnen Year Shegu Dashi Har Takai Ga Sun Lakada Masa Duka Da Ya Kai Ga An Kwantar Dashi Asibiti Domin Samun Lafiya

A Farkon Watan Janairu Na Wannan Shekara Da Muke Ciki Mr James Mugo Ya Nemi Duk Wani Mutum Dake Yin Ibada a Cocinsa Da Ya Tabbatar Da Ya Biya Ksh 4200 Idan Har Yanason Samun Albarkar Sabuwar Shekara Idan Kuma Ba Haka Ba Mutum Ba Zai Yi Albarka Ba,Hakan Da Malamin Ya Fadi Ya Fusata Ran Jama’ar Dake Cikin Cocin Har Takai Ga Sun Dauki Mataki

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button