HausaUncategorized

Masarautar Gumel Ta Kayyade Kayan Da Zaa Saka A Kayan Lefe

Masarautar Gumel dake Karamar Hukumar Gumel A Jihar Jigawa Ta Kayyade Kayan Da Zaa dinga Sakawa Acikin Kayan Lefe saboda saukaka ma Matasa yin Aure ba tare da Tsawwalawa Ba Inda Suka Rubuta Kayadaddun Kayan Da Duk Wani Mai Nufin Yin Aure A Masarautar Amma Ta kumace Sadaki Zai Kasance Daidai Da Yanayin Karfin Mutum

Takardar Sanarwa

Kamar yada Masarautar ta Gumel Ta Rubuta a cikin takardar

Gaisuwa da Fatan Alheri dangane da takardar da muka Samu Daga Karamar Hukumar Gumel Akan dokar kayyade Kayan Aure ta Ranar 2/10/2021 Muke sanar da dukan limaman Juma’a Da su sanar da Jamaa a cikin hudubar su ta Sallar Juma’a Kan Wannan doka ta aure

An Yi Wannan doka don saukaka wahalhalu da Al’adu dake tattare a sha’anin Aure Don Haka Jamaa su bada Hadin Kai da goyon Baya

Ga Jerin Abubuwan Da Aka Hana

Jerin Abubuwan Da Aka Hana

1 Ba’a Kayyade Sadaki Ba Amma Ya Kasance Yayi Daidai da Yanayin Tattalin Arzikin Yankin

2 Tufafi Kala Shida (6)

3Takalma (3)

4 Hijabi Da Mayafai (3)

5 Kayan Kwalliya seti (2)

6 An Hana Gara

7An Hana Angani Anaso

Da Sauransu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button