Hausa

Mata Sun Fara Neman Mijin Aure A Allon Talla

Aure Sunna Ce Ta Manzon Allah (SAW),Amma da Dama Wasu Basu da Aure Sakamakon dalilai Dabam Dabam Kama Daga Rashin Zarafi,Rashin Lafiya Ko Kuma Wani dalili Dabam

Mafi yanwancin Wanda zaka ga Basu da Aure Matane,Saboda Wasu Mazan sun Fi son su  Zauna da Mata Daya saboda gujema kasawa wajen daukar nauyinsu da yayan da Zasu Haifa,Wasu Matan Kuma sun yi Auren Amma Allah Ya nufi su Rabu da Mijinsu Sakamakon Wasu dalilai

Duk Matar da ta fito Gidan Mijinta Itace ake Cewa Bazawara,A Wannan Lokacin Da Wadanda Basu yi Aure ba ma sun rasa Mazajen Aure balantana Bazawara da ita Tayi Aure ta fito

Sakamakon haka Yasa Mata Marasa Aure Sukayi Yawa A Cikin Alumma Kuma Suna bukatar Aure Amma Basu Samu Mazajen Aure ba

Hakan Yasa Wasu Matan Suke Neman Mazajen Aure ta kowace hanya Saboda gujema saba ma Allah,daga cikin Hanyoyin Neman Mijin har da Tallatawa A Allon Talla

Allon Talla

Allon Da Aka yi ma Rubutu kamar haka

Haj Amina Ahmad Mai Dalilin Aure Bazawara,Budurwa,Juya Da Mace Mai Gidan Kanta

Bayan haka Kuma Allon Yana Dauke da adireshi da Kuma lambar wayar da zaka Kira idan har kana bukatar Auren Daya daga cikin Nau’in Matan Da Aka Rubuta

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button