Hausa

Matasa Sun Kona Motar Giya Don Nuna Fushi Akan Hare Haren Yan Bindiga A Yankinsu

Fusatattun Matasa A Garin Bena Dake Karamar Hukumar Danko Wasagu A Jihar Kebbi sun Kona Wata mota dauke da Giya Domin su Nuna fushin su Akan Abin dake faruwa a Yankinsu na hare Haren Yan Bindiga dake Ke Kara taazara a Yankin

Mai Magana Da Yawun Matasan Bashar Abdulhamid ya Fada ma wakilin mu Cewa sun yi sati biyu Suna sintiri a Kan titunan Garin nasu Inda Suke Duba Motoci da babura dake wucewa Akan titunan garin,ya Cigaba da Cewa Wani Mutum ne yazo da Mota makare da Giya Wanda su Kuma suka dauki Matakin konawa da kuma kama wanda ya ce Giyar Tasa Ce

Giyar Da Aka Kona

Munyi hakane domin Hana Bata Garin Mutane su kaiwa Yan Ta’adda Kayan Maye Da ire irensu Inji Shi

Yankin Karamar Hukumar Danko Wasagu na fama da hare Haren yan Bindiga A Yan Kwanakin Nan Inda Sama da Mutum 10 suka rasa rayukan su a sati biyu da suka gabata

Yanzu Haka Dai Gwamnatin Jihar Kebbi Karkashin Jagorancin Sen Atiku Abubakar Bagudu Ta Hana yawo da babura Daga karfe 7 na dare Zuwa karfe 6 na Safiya

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button