Hausa

Mawaki Nura M Inuwa Ya Zama Gwarzon Mawakin Shekara

Shahararren Mawakin Fina Finan Kannywood Nura M Inuwa Ya Zama Gwarzon Mawakin Shekara Bayan Da Makarantar Koyon Ilimin Addinin Musulunci Da Sauran Darusa Ta Aminu Kano Ta Karramashi Da Kyautar Gwarzon Mawakin Shekara

Kyautar

Nura M Inuwa Ya Kasance Daya daga cikin Mawakan da tauraruwar su ta Dade Tana Haskawa a Masana’antar ta Kannywood Inda ya zamo Mutum Na Farko da ya Fara yin Album Mai dauke da wakoki Fiye da Goma A Tarihin Masana’antar Kannywood

Kafin Wannan Karramawar Nura Ya Samu lambobin Yabo Da dama daga ciki Akwai Best Artist na City People Music Award Wanda Ya Kasance Kyauta Mafi Daraja Ga Duk Wani Mawakin Kannywood

Nura Mawaki Ne Da Ya Mayar da hankalinshi Akan Wakokin Soyayyar Wanda Kuma Hakan ya Janyo Masa masoya da dama Musamman Matasa Wadanda suka Fi sauraron wakokinsa,Bayan Wakar Soyayya a Fina Finai Yana Kuma Wakar Aure,Suna, Birthday Da Kuma Siyasa

Nura M Inuwa

Karramawar Da Makarantar Tayi Masa Yasa Ya Zama Mawaki Na Farko Da Makarantar Ta Taba Bawa Wata Kyauta A Hukumance

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button