Wasanni

Munfi Samun Dama Yanzu Akan Lokacin Rohr-Simon Moses

Dan Kwallon Tawagar Super Eagles Ta Najeriya Dake Fafatawa a Gasar Cin Kofin Afirka A Kamaru Moses Simon Ya Bayyana Cewa Sunfi Samun Dama Yanzu Da Koci Eguevon Yake Jagorancin Kungiyar Akan Lokacin Da Tsohon Koci Genort Rohr Yake Jan Ragamar Tawagar

Moses Simon

Simon Wanda Yayi Fira Da Yan Jarida Bayan Tashi Wasan Da Najeriya Tayi Nasara Akan Kasar Sudan Da Ci 3-1 Ya Ce Lokacin Rohr Muna Bin Umar in Shine Kawai,Yanzu Kuma Wannan Kocin Yana Bamu Damar Amfani Da Kwarewarmu Wajen Taka Leda Ba Tare Da Wata Tsangwama Ba

Najeriya Wacce Take Group D Tareda Egypt,Sudan Da Kuma Guinea Bissau Ta Kai Zagaye Na Gaba Bayan Doke Kasar Sudan Wanda Hakan Yasa Ta Zama Kasa Ta Biyu Da Ta Yi Nasara A Dukkan Wasannin Da Ta Buga Bayan Kasar Kamaru Mai Masaukin Baki

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button