"
Hausa

Mutuwar Hanifa-Iyaye Suna Zuwa Tun Kafin A Tashi Makaranta Don Daukar Yayansu

Tun Bayan Mummunan Kisan Da Wani Malamin Makaranta Mai Suna Abdulmalik Tanko Yayiwa Dalibarsa Hanifa Abubakar A Kano Iyaye Na Zaman Dar dar A Wajen Zuwan Yayansu Makaranta Musamman Yara 

Wani Malamin Makaranta Da Wakilinmu Ya Zanta Dashi ya Tabbatar Da Cewa Yanzu Iyaye Na Zuwa Makaranta Tun Kafin A Tashi Domin Su Dauki Yayansu da Kansu Don Gujewa Abin Da Ka Iya Zuwa Yadawo

Tun Bayan Kisan Da Wani Malamin Makaranta Yayiwa Dalibarsa Hanifa Abubakar A Kano,Iyaye Ke Taka Tsantsan Wajen Ganin Yaransu Sun Samu Isasshen Tsaro A Makarantu

Hakan Yasa Wasu Ke Tabbatar Da Sun Isa Makaranta Da Wuri Kafin Tashin Daliban Domin Su Dauka Yayansu Da Kansu,Wanda Hakan Ya Rage Ma Malamai Hidimar Kula Da Yaran Bayan An Tashi Daga Makaranta

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button