Hausa

Noma Tushen Arziki- Yada Manoman Garin Bena Suka Fara Cin Gajiyar Nomansu

Noma Tsohon Ciniki Kowa Yazo Duniya Kai ya Tarar Haka Masu iya Magana suka fadi,Kuma Wannan ba karya Bane Domin Kuwa Noma ya Kasance Daya Daga Cikin Sanao’in Da Suka Dade Ana Yi Fiye Da Shekaru Dari A Fadin Duniya

Babu Inda Ba’a Noma A Fadin Duniya,Anayin Noma A Kowace Kasa Kuma A Kowane Lungu Da Sako A Duniya

Kasuwar Buhu A Garin Bena

Kasar Thailand Tafi Kowace Kasa Noman Shinkafa A Duniya Ita Kuma Najeriya An Santa Da Noman Gyada,Alkama Da Sauransu,Birni Da Kauyuka Ana Noma A Najeriya

Daya Daga Cikin Yankin Da Akafi Maida Hankali Wajen Noma Shine Yankin Bena Dake Karamar Hukumar Danko Wasagu Ta Jihar Kebbi

Yanki ne Dake Da Tarin Manoma Da Kuma Yan Kasuwa Suna Makwabtaka Da Jihar Neja Daga Kudanci Sai Kuma Jihar Zamfara A Gabaschi,Garin Bena Garine Wanda Allah Ya Albarkata Da Kasar Noma Mai Tarin Yawa,NomaHasashe Ya Nuna Suna Noma Hatsin Da Zai Iya Ciyar Da Jihar Baki Daya A Shekara Daya

Suna Alfahari Da Wannan Baiwa  Da Ubangiji Yayi Musu ,Suna Da Kasuwar Da Suke Kai Albarkatun Nomansu Da Suka Noma Duk Sati Inda Ake Cin Kasuwar Duk Ranar Lahadi,Kuma Mutane Daga Sassa Dabam Dabam Ke Zuwa Domin Kasuwanci

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button