Wasanni

Shahararren Dan Kwallon Kafar Duniya Ya Ajiye Takalminsa

Wani Abu Da Ya Faru Kamar Almara Shine Sanarwar Da Shahararren Dan Kwallon Kafar Argentina Da Barcelona Sergio Kun Aguero Yayi Na BarinĀ  Kwallon Shi Sakamakon Ciwon Zuciya Da Yake Fama Dashi

Kun Aguero Yayin Da Yake Bankwana Da Kwallo

Shidai Aguero Ya Shahara A Fagen Tamaula A Fadin Duniya Inda Har Takai Ga Ana Hasashen Yana Daga Cikin Yan Wasan Da Suka Iya Zura Kwallo A Raga

An Haifi Aguero A Ranar 2 Ga Watan Yuni A Babban Birnin Argentina Buinos Aires,Ya Fara Bugawa Kungiyar Kwallon Kafa Ta Independent Dake Argentina Kafin Ya Tsallako Zuwa Turai Inda Ya Bugawa Kungiyar Kwallon Kafa Ta Athletico Madrid Dake Sifen Wasa,Zuwanshi Manchester City Yasa Duniya Ta Kara Saninshi Kuma Ya Kara Samun Tagomashi A Harkar Kwallon Kafa

Aguero

Aguero Ya Bugawa Manchester City Wasa 275 Inda Ya Jefa Kwallo 184 A Zaman Da Yayi A Manchester,Yana Daga Cikin Yan Wasan Da Kasar Argentina Ta Buga Kofin Copa America Wanda Ta Lashe A Shekarar Nan,Ya Bugawa Kasarsa Wasa 101 Da Kuma Zura Kwallaye 41 A Raga

Wasansa Na Karshe A Harkar Kwallon Kafa Shine Wanda Kungiyar Kwallon Kafa Ta Fc Barcelona Ta Hadu Da Abokiyar Hamayyarta Wato Real Madrid Wanda Kuma Aguero Shine Ya Jefa Wa Barcelona Tilon Kwallon Da Suka Jefa A Karawar

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button