"
Hausa

Wani Da Ba’a San Kowanene Ba Ya Banka Wa Motar Sarkin Garinsu Wuta

Wani Mutum Da Ba’a San Ko Wanene Ba ya Bankawa Motar Sarkin Garin Mai Rai Rai Dake Gundumar Bena A Karamar Hukumar Danko Wasagu Dake Jahar Kebbi Wuta Kuma Ya Arce Ba Tare Da An Kamashi Ba

Motar Sarkin Mai Rai Rai Da Aka Kona

Dagacin Dan Ummaru Ya Hadu Da Iftila’in Konewar Mota Bayan Da Wani Ya Banka Mata Wuta Ya Arce Ba Tare Da Wani Ya Ganshi Ba Da Yake Amsa Tambatar Wakilinmu Dagacin Ya Ce Shi Baya Zargin Kowa Akan Wannan Al’amari Da Ya Faru Dashi Inda Ya Danganta Abun Da Jarabawa Daga Allah Kuma Ya Barma Allah

A Wasu Lokutan Sarakuna Musamman Na Karkara Na Haduwa Da Makiya Da Dama Inda Suke Nuna Adawarsu Da Sarakunan A Fili Ba Tare Da Wani Boye Boye Ba,Hakan Na Faruwa Ne Saboda Bacin Rai Da Sauran Dalilai

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button