Hausa
Wani Gwamna A Arewa Ya Tsaya Ya Sayi Waina Akan Hanya

Hotunan Gwamnan Jihar Borno Prof Babagana Umara Zulum Ya Tsaya A Bakin Hanya Inda Ya Sayi Waina Da Miya Cikin Girmamawa ba Tare da Jamian Tsaro Ba Ya Karade Kafafen Sada Zumunta

Gwamnan Wanda Ya Fita Da Sanyin Safiya Ya Taka A Kasa Ya Tafi Har Inda Ake Tuyar Waina Da Miya A Bakin Titi Ya Saya Aka Saka Masa A Leda Yayi Tafiyarsa

Mutane Sunyi Ta Tofa Albarkacin Bakinsu Akan Wannan Abu Da Gwamnan Yayi Inda Wasu Ke Cewa Irinsu Babagana Umara Zulum Ya Kamata Su Mulki Jamaa Tunda Basuda Girman Kai Ko Tsangwama
Gwamnan Yasha Nuna Al’amuran Da Yake Nuna Tsantsar Son Jama’a Da Rashin Girman Kai