"
Hausa

Yajin Aikin Adaidaita A Kano- Anyi Asarar Naira Biliyan Daya A Kwana Daya

Ranar Litinin 10 Ga Janairun 2022 Kungiyar Masu Adaidaita Sahu Ta Jahar Kano Suka Fada Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Sakamakon Abin da Suka Kira Takurawar Da Karota Suke Masu

Dan Adaidaita A Bakin Aiki

Yajin Aikin Wanda Ya Fara Jiya da Safe Ya Tsayar Da Harkar Zirga Zirga A Kano Inda Mutane Da Dama Suka Yi Tafiya A Kafa Zuwa Wajen Aiki Da Kuma Sauran Wurare,Masu Adaidaita A Kano Zasu Kai Mutum 200,000 Shine Masana Sukayi Hasashen Cewa Duk Mutum Daya Zai Iya Samun Karanci Naira 5000 A Wuni Daya,Wanda Hakan Yasa Anyi Asarar Naira Biliyan Daya Cikin Kwana Daya

Shugaban Hukumar Kula Da Ababen Hawa Ta Jahar Kano(KAROTA)Baffa Dan Agundi,Ya Bayyana Wannan Yajin Aiki A Matsayin Bata Lokaci Da Yan Adaidaita Sahun Keyi,Inda Ya Cigaba Da Cewa Duk Tsawon Lokacin Da Zasu Dauka Suna Yajin Aiki Sai Sun Biya Haraji Koda Basu Fito Aikiba

Mutanen Jahar Kano Na Burin Ganin Ranar Da Za’a Sasanta Tsakanin KAROTA Da Yan Adaidaita Domin Cigaba Da Zirga Zirga Kamar Yada Aka Saba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button