Hausa

Yanzu Yanzu- Gwamnatin Tarayya Ta Mikawa Pantami Zunzurutun Kudi Domin Rufe Layuka

Majalisar Zartarwa Da Ta Zauna Jiya Laraba A Fadar Shugaban Kasa  Ta Amince Da Cire Zunzurutun Kudi Har Naira Biliyan 1.8 Domin Rufe Duk Wasu Layukan Waya Da Ake Amfani Dasu Wajen Kwarmata Bayanai Ga Yan Bindiga Da Sauran Ayyukan Laifi A Fadin Najeriya

Ministan Sadarwa Dr Ali Isa Pantami

Majalisar Wadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Jagoranta Ta Amince Da Fitar Da Wannan Kudi A Kokarinta Na Dakile Ayyukan Ta’addanci Da Sauran Laifukan Da Ake Amfani Da Layukan Waya Wajen Aikatawa

Ministan Sadarwa Dr Ali Isah Pantami Ya Bayyana Wannan Mataki A Matsayin Wata Hobbasa Da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari Yakeyi Wajen Dakile Ayyukan Ta’addanci A Fadin Najeriya,Ya Kuma Bada Tabbacin Yin Aikin Tukuru Da Wannan Kudi Wajen Ganin An Cimma Abin Da Ake Nema

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button