Hausa
Zamu Cigaba Da Gwagwarmayar Musulinci A Najeriya-El Zakzaky

Shahararren Malamin Addinin Musulinci Kuma Shugaban Islamic Movement A Najeriya Sheikh El Yakoub Ibrahim El Zakzaky Yace Zasu Cigaba Da Gwagwarmayar Musulinci Har Iyakar Rayuwarsu

Malamin Wanda Gwamnatin Najeriya Karkashin Jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari Ta Tsare Tsawon Shekaru Da Dama Ya Fadi Cewa Shi Da Mabiyansa Bazasuyi Kasa A Gwuiwa Ba Wajen Tabbatar Da Wanzuwar Musulinci A Najeriya Ba
Gwamnatin Najeriya Ta Zargi Jagoran Shi’ar Da Yunkurin Tayar Da Tarzoma A Lokacin Da Mabiyansa Suke Taronsu a Zaria Wanda Hakan Yasa Take Tsare Dashi Tun Shekarar 2015 Kafin Ta Sako Shi A Shekarar Da Ta Gabata